Wednesday, 30 November 2016

HARKOKIN BIZINES 5 DA ZA KA ItYA FARA SU GOBE

Harkokin bizines guda 5 da za ka iya fara su gobe
Bayar da dukkan lokaci ga yin aiki wani babban lamari ne mai dauke hankalin duk wanda yake son ya soma wata karamar harkar kasuwanci mai riba. Haka lamarin yake idan kana tafiyar da wata harkar kasuwanci mai jan lokaci, kuma ba ka da damar tantance wane abu ne kuma za ka iya sa kanka ciki.
A yayin da yawancin mutane suka yi amannar cewa mutanen da ke da sa’a, kudi, hazaka ko baiwa ne kawai kan iya zama masu sana’ar kansu, ba sa la’akari da cewa sun kasa fara sana’ar kansu ne saboda imanin da suka yi cewa masu sana’ar kansu da suka yi fice sun fara ne daga babban matsayi, don haka sai suke dabaibaye kansu cikin tsarin aiki na daga karfe 9:00 na safe zuwa karfe 5:00 na yamma a kullum.
In ka samu kanka makale cikin tsoron fara sana’ar kanka, ko ka kasa samun harkar bizines da za ka soma da jarin da kake da shi, to ga wasu kananan harkokin bizines da za ka iya fara su ma gobe-goben nan:

1) Yi wa mutane hidima
Harkar yi wa mutane hidima wata harkar bizines ce da ake wa mutanen da suke da karancin lokaci zuwa rashin lokacin da za su yi kanana amma muhimman ayyuka. Za a iya aiwatarwa ta hanyar taimakon mutum zuwa yi masa siyayya a kasuwa, taimaka musu yin wankau, taimakawa iyali tashi daga gida zuwa wani gidan, yin shara a gida da sauransu.
Tunda kuma yawancin masu bukatar irin wannan hidima daga ajin ma’aikata ne, wadanda ba su da lokacin yin wadannan kananan muhimman ayyuka, yin hayar mutum biyu masu yi maka aiki da tallata hidimarka ga ajin wadancan mutane a ofisoshinsu, gidaje, da wuraren hutawarsu zai iya samar maka da kwastomominka cikin kankanen lokaci.
2) Wasannin bidiyo da na kwamfuta
A kasa kamar Nijeriya, da yawan ’yan makarantar Sakandare ba sa samun damar yin isasshen wasannin kwamfuta (gem). A yayin da wasunsu suke da gatan mallakar gem na bidiyo a gida, da yawansu kuwa suna zuwa gidajen gem da zarar an tashi makaranta don yin gem din da suka fi so, yawanci kuma na kwallo ko playstation ko xbox.
Idan kana da gem na bidiyo da kuma ’yan kudi kadan da za ka iya hayar karamin shago kusa da makarantar Sakandare, to za ka iya soma wannan bizines din a gobe ma.
 3) Fara sai da kayan kamfani
A yayin da wata harkar kasuwanci ta bunkasa, tana samun tudadan kwastomomi, sai ka ga tana bunkasa cikin sauri zuwa larduna, kuma a yayin haka nan, sai ka ga tana sai da damar sai da kayayyakinta ga masu shirin tallata hajarta. Ba kamar fara sabon bizines ba, sayen damar sai da kayan kamfani yana iya zama mai tsada, musamman da yake akwai ka’idojin da kamfani ke shimfidawa wadanda dole ka cika su a koyaushe.
Idan kana da isassun kudin da za ka iya sayen damar sai da kayan kamfani, to za ka iya samun kudin shiga mai yawa tun a ranar farko da ka bude shagonka, tunda za ka samu yawancin mutane sun aminta da irin kayan kamfanin.
Misali shi ne sayen damar sai da kayan kamfanin KFC. Tunda kayan kamfanin ya shahara da mutane suka san shi, to za ka soma samun riba da zaran sito dinka na KFC ya soma aiki.
4) Gidan Cin Abinci
Gidajen sai da abinci, ko ‘Mama Put’ kamar yadda suka shahara da sunan a Nijeriya, wani harkar bizines ne da zai iya cika aljuhunka da kudi tun a ranar farko da ka fara.
Mutane da dama suna neman gidajen cin abinci mafi kusa da su, inda za su samu abincin da za su ci cikin hanzari kuma da araha. Haka kuma masu haya da babura sukan dunguma ga ire-iren wadannan wurare don yin kalacin safe, cin abincin rana, wani lokaci ma har da na dare.
Sabanin manyan gidajen cin abinci da suke cazan kudi da yawa kan abincinsu, irin wadannan kananan gidajen cin abinci suna cazar kwastomominsu kudi kadan da ya gaza da kusan nunki uku na manyan gidajen cin abinci, wanda hakan kuma ke jawo musu sha’awar mutanen da suke kewaye da su.
 5) Ba da shawara kan harkokin Dandalin sada zumunta
Idan kana hulda da Dandalin sada zumunta na zamani sosai, kuma kana da masu bin ka da yawa da zai burge kowa, to za ka iya fara harkar bizines ta ba da shawara a kan Dandalin sada zumunta gobe-goben nan!
Da fari dai ka yi bincike sosai kan irin hajojin da ke akwai da kuma irin huldar da suke yi da Dandalin sada zumunta. Sai ka gano wadanda ba sa hulda din sosai da sosai, amma suke da damar samun habakar kasuwancinsu in da za su yi hulda da Dandalin sada zumunta sosai, sai ka tuntube su kan hakan.
Zai fi sauki ka fara da wadanda yanzu suka soma hulda da Dandalin sada zumunta. Sune za su iya zama fandishon da za su zama tsaninka na isa ga manyan kamfanoni a nan gaba.
Mene ne ra’ayinka kan wadannan harkokin bizines guda biyar da za ka iya somawa a goben nan? Za mu so jin ra’ayinka ta hanyar ziyartar shafinmu a intanet mai adireshi kamar haka: www.dabarunbizines.blogspot.com
Ko kuma shafinmu na facebook mai adireshi kamar haka: www.facebook.com/dabarunbizines
Ko kuma ta imel ]inmu: dabarunbizines@gmail.com
Ga kuma lambar wayarmu: 0815 020 9637
Har ila yau wannan Dandali na Dabarun Bizines yana ba da shawarwari ga duk mai bukatar fara kowace irin harkar bizines kan farashin N200 kacal. Katin MTN na N200 za ka turo ta layinmu: 0815 020 9637 tare da Sunanka, garinku, da irin bizines din da kake son yi, mu kuma za mu shirya maka dabarun fara bizines din mu turo maka ta imel ko whatsapp ko facebook messenger dinka cikin kankanen lokaci.
Ka jarraba ka gani! Himma ba ta ga raggo!!

No comments:

Post a Comment