Wednesday, 7 December 2016

Bizines 10 masu riba da za ka iya farawa daga dakinka



Bizines 10 masu riba da za ka iya farawa daga Dakinka
A da, fara duk wani bizines yana tattare da hayan babban ofis, hayar ma’aikata, biyan wasu kudaden ka’ida da sauransu. Ba tare da la’akari da cewa ko bizines din da aka fara zai janyo riba ba ko a'a, dole mutum ya bi wadannan matakan kafin mutane su san da gaske yake yi, kar su zaci dan damfara ne.

A yayin da wadannan matakan na kashe kudi suke aukuwa a da can, yanzu yana kara zama cikin sauki kuma tare da riba, mutum ya fara bizines daga gida fiye da a kowane lokaci.
Yanzu mutane sun fi aminta kan abin da suke biya, ko da ko ba su yi ido biyu da mutum ko kayan ba. Sun yi amanna cewa za su samu abin da ya yi daidai kudinsu, kuma ya fi sauki da kuma arha ka yi hulda da bizines din da ke biyan bukata yadda ya kamata, ba tare da la’akari da inda ofis dinsu yake ba.

Idan kana tunanin ka fara wani bizines daga gida, amma ka kasa samun tsayayyar shawara, to ga wasu harkokin bizines guda goma da za ka iya fara su daga dakinka:

1) WANKI DA GUGA:
Wanki da guda, za ka iya fara shi daga gidanku ma.Tunda yawancin mutane ba su da lokacin yin wankin kayansu, musamman maza, wadanda dama malalata ne in an soma batun wanki. Damar da wannan hidima za ta bayar na da yawan gaske.

Za ka soma daga unguwarku, ta hanyar barin mutane su san cewa kana yin wankau. Don jawo ra’ayin jama’a ga hidimarka kana iya rangwanta farashin naka wankau din in an kwatanta da na sauran masu wankau a unguwarku, ta yadda zaka iya samun wani kaso mai girma daga kasuwar wannan harkar bizines din.

2) DAUKAR HOTO
Daukar hoto wata sana’a ce da ba ka bukatar ka bude situdiyo kafin ka fara ta. Wannan harkar bizines din tana da fadin gaske, ta yadda daidaiku, musamman dalibai, suna taka muhimmiyar rawa a cikin ta.

Wasu daga cikin masu daukar hoton suna daukar hoton abinci ne kawai, wasu jarirai kawai, wasu bukukuwan aure, wasu iyalai, wasu yanayin gari ko kasa da sauransu dai, kuma suna tallata hidimarsu ta hanyar shafukan hotuna na intanet, inda suke nuna ingancin hotunansu da suka dauka.

Duk da cewa wasu bangarorin daukar hoto a wani lokaci zai bukaci ka mallaki naka situdiyon da ya dace, amma wasu kwararrun masu daukar hoto ba su da shi, maimakon haka sukan dauki hotunansu ne su sayar a shafukan sai da hotuna na intanet.

A duk lokacin da wani ya sayi hoton da suka dora a shafin intanet, sai a biya su. Cinikin da suke yi kan bunkasa ya kai samun Dala 1,000 zuwa 5,000 a wata, gwargwadon ingancin hotunan da kuma yadda suka iya ja hankalin jama’a da gamsar da bukatun masu saye da dama.

Wasu shafukan sai da hotuna da zaka iya sayar da hotunanka sune: www.depositphotos.comwww.dreamstime.comwww.shutterstock.com da sauransu.

3) HARKAR SUFURI
Jama’a da dama masu shiga harkar ba da hayar kayayyakin sufuri, sukan gamu da matsalolin lura da direbobi, tabbatar da cewa suna biya a kan kari, da kama su da laifin ayyukansu da kan shafi motoci ko baburan da suke amfani da su.

Za ka iya dauke wa masu motoci ko Babura irin wannan damuwar ta hanyar tafi da harkar bizines din kula da harkokin sufuri. A nan ba kawai zaka yi hayar direbobi ba ne ga kwastomominka, za kuma ka lura da su, ka tabbatar da cewa hakkokin kwastomominka na zuwa kan kari, kuma ka fitar da wani tsarin lura da motocinsu, wanda zai ba su damar sa ido kan motocinsu ko baburansu.

Su kwastomomin za su rika biya ne kan kowane abin hawa da ake kula musu da shi. Kuma idan za ka lura da ababen hawa dari a wata, misali a kan N10,000 kowane wata, ai ka ga zaka samu Naira miliyan daya ke nan kowane wata.

4) SHIRYA WURI
Harkar shirya wuri da kawata shi wata babbar harkar bizines ce a Nijeriya. A kowace ranaba ka rasa wani buki da ake yi a wani wuri inda jama’a da dama kan taru. Tsara wuri don gudanar da wani buki na bukatar shiri sosai, shi ya sa mutane kan nemi hidimar kwararrun da suka iya shirye-shirye, kuma mutane suka shaida.

Za ka iya shiga wannan harkar ka taka rawa wajen shirya bukukuwan kamfanoni, daurin aure da sauran muhimman tarurruka.
5) DAKON ABINCIN
Harkar dakon abinci a Nijeriya, kodayake sabon abu ne, amma ana yin sa a wurare da dama. A yayin da wasu suka fi mai da hankali kan dakon abincin da kwastomomi suka yi oda daga gidajen cin abinci daban-daban, sai aka bar wani gibi na samar da kalaci ga kamfanoni da Ma’aikatu.   

Abin da ke faruwa shi ne maimakon mutane su fita yawon neman abincin da za su ci a kullum, za ka iya yi wa kamfanoni tayin cewa za ka rika samar musu da abincin rana na ma’aikatansu a kullum a kan wani kayyadadden lokaci.

Don ganin wannan hidima taka ta samu karbuwa, dole ka rika samar da abinci mai dadi kuma wanda ya fi na gidajen abinci arha, kuma ka tabbatar kana samar da su a kan lokaci a koyaushe.

In ka wadatar da wata Ma’aikata, sai ka matsa ga na gaba; haka-haka har ya zama kana da jerin kamfanonin da kai kake samar musu da abincin ranarsu a kullum.

Hidimar dakon abinci wani bizines ne da za ka iya yin sa daga gida ba tare da ka yi hayar wani babban ofishi ba.

6) YI WA JAMA’A KWALLIYA 
Yi wa jama’a kwalliya wata baiwa ce. Akwai dalilin da ya sa da yawan mata ba sa iya nuna kwarewa a harkar yin kwalliya kamar yadda kwararru suke yi.

Idan kina da baiwar yin kwalliya, to kina iya shiga makarantar ba da horo kan yin kwalliya don ki inganta baiwarki. Daga nan sai ke ma ki rika yi wa jama’a, musamman amare masu shirin yin biki na aure da sauransu.

In kin nuna kanki a matsayin dwararriyar mai yin kwalliya, mutane za su rika gayyatar ki zuwa gidajensu, ofisoshinsu da sauransu don yi musu kwalliya saboda bukukuwan da ke gabansu a kan wasu ’yan kudi. Kuma ya fi riba idan jama’a suka fahimci kin kware a wajen yi wa Amare kwalliya ne, don ba karamin kudi ake kashewa kan hakan ba.

7) YIN KAMU DA KOSTAD
Bukatar kamu ko gasara ko kullin koko da kostad a Nijeriya na da yawa sosai. Da yawan mutane suna shan koko ko dama kamu, wasu da safe, wasu da maraice, wanda ake siyowa daga masu talla ko masu sai da kosai ko akara.

Za ka iya fara bizines din yin kamu ko dama kostad, ka yi masu mazubi na musamman ka raba wa manyan shagunan saide-saide da sauran ’yan tireda.

8) YIN ZANE DA KWAMFUTA     
Yin zane-zane da kwamfuta wani bizines ne da bai bukatar mai yin sa ya bar gidansa. Wannan bizines da zaka iya yi a gida ana yin sa ne kawai daga kwamfutar mai yin zanen, sannan a tura wa kwastoma ta imel.

Idan kana da manhajar Adobe photoshop da sauran manhajojin yin zane da kwamfuta, to zaka iya fara wannan harka ta zane-zane da kwamfuta.

Da farko dai ka tabbatar cewa shafinka na zane-zane na intanet yana da jan hankali, daga nan ne zaka rika tallata ayyukanka ga zaurukan jama’a tare da hada gwiwa da sauran masu zane-zane don cimma kasuwar.

9) TALLA TA DANDALIN SADA ZUMUNTA
Duk wanda yake da mabiya da maziyarta shafinsa a Dandalin sa da zumunta a intanet, to zai iya fara tafiyar da bizines na yin talla. Irin ayyukan da kake yi a shafinka, wanda shi ya samar maka da mabiya masu yawa, zai iya b aka damar tallata kwastomomi masu yawa.

Yin talla ta Dandalin sada zumunta wani babban bizines ne daga gida, kuma daga dakinka. Abin da kawai kake bukata shi ne yawan mabiya da kuma wasu dabaru na iya tallata kwastomominka. 

In ka shirya sosai, zaka ma iya tuntubar kwastomominka ta waya, ka yi magana da su kan yadda zaka iya inganta hajarsu a Dandalin sa da zumunta, ka nuna musu inda za su samu ayyukanka a shafukan intanet, da ma yi musu tayin ba su ala-koro na hidimarka.

10) SAMAR DA SOYAYYEN AYABA DA DANKALIN TURAWA
Soyayyar ayaba da dankalin Turawa wani abinci ne da ake yawan cin sa a kullum a Nijeriya. Soyayyen ayaba, wani abincin ci nan take ne da ake bukatarsa, musamman ake yawan sayen sa a inda ake yawan samun cunkoson ababen hawa.
Kuna iya soya dankalinku, ku yi masu mazubi mai kyau, ku ba ’yan talla wadanda za su sayar kai tsaye ga masu ababen hawa da fasinjoji da shagunan sai da kayayyakin yau da kullum. Wannan bizines din na daya daga cikin harkokin da jama’a da dama suka kasa cin gajiyarsa.

Mene ne ra’ayinka kan wadannan harkokin bizines guda goma da za ka iya somawa daga dakinka?

Za mu so jin ra’ayinka ta hanyar ziyartar shafinmu a intanet mai adireshi kamar haka: www.dabarunbizines.blogspot.com

Ko kuma shafinmu na facebook mai adireshi kamar haka: www.facebook.com/dabarunbizines
Ko kuma ta imel dinmu: dabarunbizines@gmail.com
Ga kuma lambar wayarmu: 0815 020 9637

Har ila yau wannan Dandali na Dabarun Bizines yana ba da shawarwari ga duk mai bukatar fara kowace irin harkar bizines kan farashin N200 kacal. Katin MTN na N200 za ka turo ta layinmu: 0815 020 9637 tare da Sunanka, garinku, da irin bizines din da kake son yi, mu kuma za mu shirya maka dabarun fara bizines din mu turo maka ta imel ko whatsapp ko facebook messenger dinka cikin kankanen lokaci.
Ka jarraba ka gani! Himma ba ta ga raggo!!

Wednesday, 30 November 2016

HARKOKIN BIZINES 5 DA ZA KA ItYA FARA SU GOBE

Harkokin bizines guda 5 da za ka iya fara su gobe
Bayar da dukkan lokaci ga yin aiki wani babban lamari ne mai dauke hankalin duk wanda yake son ya soma wata karamar harkar kasuwanci mai riba. Haka lamarin yake idan kana tafiyar da wata harkar kasuwanci mai jan lokaci, kuma ba ka da damar tantance wane abu ne kuma za ka iya sa kanka ciki.
A yayin da yawancin mutane suka yi amannar cewa mutanen da ke da sa’a, kudi, hazaka ko baiwa ne kawai kan iya zama masu sana’ar kansu, ba sa la’akari da cewa sun kasa fara sana’ar kansu ne saboda imanin da suka yi cewa masu sana’ar kansu da suka yi fice sun fara ne daga babban matsayi, don haka sai suke dabaibaye kansu cikin tsarin aiki na daga karfe 9:00 na safe zuwa karfe 5:00 na yamma a kullum.
In ka samu kanka makale cikin tsoron fara sana’ar kanka, ko ka kasa samun harkar bizines da za ka soma da jarin da kake da shi, to ga wasu kananan harkokin bizines da za ka iya fara su ma gobe-goben nan:

1) Yi wa mutane hidima
Harkar yi wa mutane hidima wata harkar bizines ce da ake wa mutanen da suke da karancin lokaci zuwa rashin lokacin da za su yi kanana amma muhimman ayyuka. Za a iya aiwatarwa ta hanyar taimakon mutum zuwa yi masa siyayya a kasuwa, taimaka musu yin wankau, taimakawa iyali tashi daga gida zuwa wani gidan, yin shara a gida da sauransu.
Tunda kuma yawancin masu bukatar irin wannan hidima daga ajin ma’aikata ne, wadanda ba su da lokacin yin wadannan kananan muhimman ayyuka, yin hayar mutum biyu masu yi maka aiki da tallata hidimarka ga ajin wadancan mutane a ofisoshinsu, gidaje, da wuraren hutawarsu zai iya samar maka da kwastomominka cikin kankanen lokaci.
2) Wasannin bidiyo da na kwamfuta
A kasa kamar Nijeriya, da yawan ’yan makarantar Sakandare ba sa samun damar yin isasshen wasannin kwamfuta (gem). A yayin da wasunsu suke da gatan mallakar gem na bidiyo a gida, da yawansu kuwa suna zuwa gidajen gem da zarar an tashi makaranta don yin gem din da suka fi so, yawanci kuma na kwallo ko playstation ko xbox.
Idan kana da gem na bidiyo da kuma ’yan kudi kadan da za ka iya hayar karamin shago kusa da makarantar Sakandare, to za ka iya soma wannan bizines din a gobe ma.
 3) Fara sai da kayan kamfani
A yayin da wata harkar kasuwanci ta bunkasa, tana samun tudadan kwastomomi, sai ka ga tana bunkasa cikin sauri zuwa larduna, kuma a yayin haka nan, sai ka ga tana sai da damar sai da kayayyakinta ga masu shirin tallata hajarta. Ba kamar fara sabon bizines ba, sayen damar sai da kayan kamfani yana iya zama mai tsada, musamman da yake akwai ka’idojin da kamfani ke shimfidawa wadanda dole ka cika su a koyaushe.
Idan kana da isassun kudin da za ka iya sayen damar sai da kayan kamfani, to za ka iya samun kudin shiga mai yawa tun a ranar farko da ka bude shagonka, tunda za ka samu yawancin mutane sun aminta da irin kayan kamfanin.
Misali shi ne sayen damar sai da kayan kamfanin KFC. Tunda kayan kamfanin ya shahara da mutane suka san shi, to za ka soma samun riba da zaran sito dinka na KFC ya soma aiki.
4) Gidan Cin Abinci
Gidajen sai da abinci, ko ‘Mama Put’ kamar yadda suka shahara da sunan a Nijeriya, wani harkar bizines ne da zai iya cika aljuhunka da kudi tun a ranar farko da ka fara.
Mutane da dama suna neman gidajen cin abinci mafi kusa da su, inda za su samu abincin da za su ci cikin hanzari kuma da araha. Haka kuma masu haya da babura sukan dunguma ga ire-iren wadannan wurare don yin kalacin safe, cin abincin rana, wani lokaci ma har da na dare.
Sabanin manyan gidajen cin abinci da suke cazan kudi da yawa kan abincinsu, irin wadannan kananan gidajen cin abinci suna cazar kwastomominsu kudi kadan da ya gaza da kusan nunki uku na manyan gidajen cin abinci, wanda hakan kuma ke jawo musu sha’awar mutanen da suke kewaye da su.
 5) Ba da shawara kan harkokin Dandalin sada zumunta
Idan kana hulda da Dandalin sada zumunta na zamani sosai, kuma kana da masu bin ka da yawa da zai burge kowa, to za ka iya fara harkar bizines ta ba da shawara a kan Dandalin sada zumunta gobe-goben nan!
Da fari dai ka yi bincike sosai kan irin hajojin da ke akwai da kuma irin huldar da suke yi da Dandalin sada zumunta. Sai ka gano wadanda ba sa hulda din sosai da sosai, amma suke da damar samun habakar kasuwancinsu in da za su yi hulda da Dandalin sada zumunta sosai, sai ka tuntube su kan hakan.
Zai fi sauki ka fara da wadanda yanzu suka soma hulda da Dandalin sada zumunta. Sune za su iya zama fandishon da za su zama tsaninka na isa ga manyan kamfanoni a nan gaba.
Mene ne ra’ayinka kan wadannan harkokin bizines guda biyar da za ka iya somawa a goben nan? Za mu so jin ra’ayinka ta hanyar ziyartar shafinmu a intanet mai adireshi kamar haka: www.dabarunbizines.blogspot.com
Ko kuma shafinmu na facebook mai adireshi kamar haka: www.facebook.com/dabarunbizines
Ko kuma ta imel ]inmu: dabarunbizines@gmail.com
Ga kuma lambar wayarmu: 0815 020 9637
Har ila yau wannan Dandali na Dabarun Bizines yana ba da shawarwari ga duk mai bukatar fara kowace irin harkar bizines kan farashin N200 kacal. Katin MTN na N200 za ka turo ta layinmu: 0815 020 9637 tare da Sunanka, garinku, da irin bizines din da kake son yi, mu kuma za mu shirya maka dabarun fara bizines din mu turo maka ta imel ko whatsapp ko facebook messenger dinka cikin kankanen lokaci.
Ka jarraba ka gani! Himma ba ta ga raggo!!