Noma
a hakikaningaskiya bai takaitu a kan nomawa da sai da kayan amfanin gona daga
tsirrai ba. Dabbobi ma ana kiwata su, kuma shi ake kira da kiwon dabbobi a
harkar noma. Don haka wannan mukala za ta mai da hankali ne kan yadda ake
farawa, tafiyarwa da kula da kiwon akuya mai riba a Nijeriya.
A
kusan kowane titi, in dai ba unguwannin rukunin gidajen gwamnati na masu hannu
da shuni ba a manyan biranen kasar nan, sai ka samu akuyoyi suna gararamba.
Jama’a da dama suna ganinwadannan dabbobi a kusan kullum, suna kuma mamakin me
ya sa masu su ke barin su suna yawo barkatai ba kula. Kodayake za ka ga ba su
da yawa, amma wadannan dabbobin suna zaman wata hanyar samun kudin shiga ga
masu kiwata su ne.
Kamar
dai kiwon kaji, kiwon kifi da sauran harkokin noma da suke samar da kudin shiga
mai tsoka idan aka yi su yadda suka dace, kiwon akuya ba kawai yana jawo kudin
shiga ba ne ga wadanda suka zuba jari a cikinsa, amma wani gagarumin harkar
kasuwanci ne ga mutanen Arewacin Nijeriya.
MENE
NE KIWON AKUYA YA KUNSA?
Kiwon
akuya shi ne kiwon nau’o’i na kuya (ko ma nau’i guda) a wani killataccen wuri
ko wata katuwar gona. Ya kuma hada da kiwon akuyoyi don bukatoci daban-daban
kamar samar da madara, nama, laka da wasu alheran daban-daban.
DAMARMAKIN
BIZINES DA KIWON AKUYOYI KE DA SHI
1).
Samar da naman akuya
A
kasashe da dama, miliyoyin mutane ne ke cin naman akuya. Saboda tsananin bukatar
sa ne ma ya sanya har akwai manyan kantunan sai da naman sa da Abbatuwa
musamman ta naman akuya a kasashe kamar Australia, Birtaniya, Indiya, Amerika
da sauran su da ake shake su da naman akuya don saidawa.
Yawan
akuyoyi a Australia yana da yawan gaske ta yadda kasar sannu a hankali ta zama
wacce ta fi fitar da akuyoyi masu rai da cimakan da ake sarrafawa daga akuya
zuwa ga kasashen duniya. Irin yadda akuya ke ja a Australia ya ba da damar
bizines sosai ga masu kiwon akuyoyi a kasar. Sai dai kuma duk da yawan akuyoyi
da kuma cimakan da ake sarrafawa daga gare su da ake fitarwa daga Australia a
kowace shekara zuwa sauran kasashe, bukatar naman akuya ba a iya cike ta ba.
A
Nijeriya ma ana tsananin cin naman akuya ta yadda akwai ma ma’aikatan da suke dokin
lokacin tashinsu aiki ya yi su garzaya gidajen shan farfesun naman akuya. Irin
yadda ake bukatar naman akuya ya sa harkar yin farfesun sa bizines ce mai
girman gaske a kasar nan. Mutane suna cin naman akuya a gida, wurin aiki,
gidajen cin abinci, walimomi da sauran wurare. Jama’a da dama in ka ba su zabin
naman da za su ci, za su ce maka naman akuya kafin ma na kaza.
Akuya
’yar durgu ita ce nau’in akuya da aka fi kiwatawa a gidaje da dama a Nijeriya.
Gidaje da dama a Kudu maso kudu da Kudu maso gabas na ks nan ita suke kiwatawa
don amfanin iyalansu da kuma saidawa a kasuwanni.
To,
a yayin da kuma yawan mutanen Nijeriya ya kai miliyan 170, sannan mutane sama
da miliyan biyar na cin naman akuya a kullum, kiwon akuya na da damar yin
harkokin bizines masu yawan gaske ga sabbin masu shiga harkar da wadanda suka
dade a ciki.
2).
Samar da nonon akuya
Cimaka
daga nonon akuya irin su yogot, madara, cuku, mai da sauransu duk ana fitar da
su ne daga nonon akuya. Wannan damar ta bizines a kiwon akuya yana samar da kudin
shiga sosai ga masu kiwon akuya a duk fadin duniya.
A
kasashe da dama, nonon akuya ana samar da shi sosai don amfanin gidaje, amma a
Nijeriya, da wuya ka samu gidan da ke shan nonon akuya, don haka kasuwancinsa
ya karanta sosai. Duk da haka, a sani, nonon akuya ya fi nonon saniya saukin
narkewa a ciki, saboda ba shi da kitse sosai. Kuma yana inganta bukatuwar cin
abinci ga mutum da kuma narkar da abinci a cikin mutum.
Yayin
da samar da cimaka daga nonon akuya ba ya ja a Nijeriya, a kasashen duniya da
dama, cimakan nonon akuya ana amfani da shi don biyan bukatar jama’a sosai.
ALFANUN
KIWON AKUYA
Ya
fi sauki ka kiwata akuya da ka kiwata kaji.
Yana
samar da aikin yi in aka yi shi yadda ya dace.
Wata
babbar hanyar samar da abinci ce.
Jarin
da ake bukata don soma shi madaidaici ne.
Aikin
da ake bukata a kansa ba yawa.
Wata
hanyar samar da taki ne mai albarka.
Ana
iya kiwata akuya a kowane irin yanayi na iska.
Dukkan
nau’in akuyoyi suna iya amfani da wuri da cimakan shanu.
Kiwon
akuya zai iya zama abin fiddawa kasashen waje.
Wata
hanya ce ta samar da sinadarin furoten na gina jiki.
NAU’O’IN
AKUYOYI
1).
’Yar durgu: Kamar yadda sunan ya nuna akuya ce da ba ta da tsawo, daf take da kasa,
an kuma fi samun ta a kudancin kasar nan. A hakikanin gaskiya ta fi samar da
nono fiye da nama, amma kuma mutanenmu sun fi kiwata ta don namanta, don yin
farfesu da sauran cimakan gargajiya.
Duk da rashin girmansu, suna samar da madara
mai inganci a kowace rana. Tatso madararsu na da wahalar gaske, amma ana iya
kiwata su a duk tsawon shekara. Kuma duk da cewa sune nau’in akuya da ya fi
samar da madara, amma wani lokaci tsadar kiwata su na da yawan gaske.
MENE
KUMA YAYA AKUYOYI KE CI?
Akuyoyi
suna kula sosai da irin abincin da suke ci. Suna sa ido sosai kan yanayin
abincinsu. Saboda yadda lebbansu suke da kuma harshensu, cikin sauki suke iya
kalmashe kananan ciyayi, kuma suna cin abubuwa da yawa da sauran dabbobin
ni’ima ba sa ci. Akuyoyi suna da halayyar cin abinci mai kyau. Suna cin abubuwa
da dama, amma kuma duk wani abinci da suka yi wa kashi ko wata dabba ta yi wa
kashi, to ba sa cin sa.
YADDA
ZA KA SOMA KIWON AKUYA: shi ne maudu’inmu na gaba insha Allah.
Za mu so jin ra’ayinka ta hanyar
ziyartar shafinmu a intanet mai adireshi kamar haka:
www.dabarunbizines.blogspot.com
Ko kuma shafinmu na facebook mai
adireshi kamar haka: www.facebook.com/dabarunbizines
Ko kuma ta imel dinmu:
dabarunbizines@gmail.com
Ga kuma lambar wayarmu: 0815 020 9637
Har ila yau wannan Dandali na Dabarun
Bizines yana ba da shawarwari ga duk mai bukatar fara kowace irin harkar
bizines kan farashin N200 kacal. Katin MTN na N200 za ka turo ta layinmu: 0815
020 9637 tare da Sunanka, garinku, da irin bizines din da kake son yi, mu kuma
za mu shirya maka dabarun fara bizines din mu turo maka ta imel ko whatsapp ko
facebook messenger dinka cikin kankanen lokaci.
Ka jarraba ka gani! Himma ba ta ga
raggo!!